Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma fadar gwamnati ta Aso Rock Villa da ke Abuja kamar yadda hadiminsa Bashir Ahmad ya sanar a Twitter.
Shugaban kasar ya je Daura a jihar Katsina ne mazabarsa domin sabunta katin rijistarsa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
Ya shafe kwanaki huɗu a garin daura inda ke matsayin mahaifar shugaban
Wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyarsa ta APC sun yi tattakin zuwa Daura domin ganawar sirri da shugaban ƙasar.