Mutane sun cika da alajabi a ranar 29 ga watan janairu 2012 a masallacin Annor inda malam fantami ke gudanar da karatu a Abuja baya da aka nemi sadaki aka rasa sakamakon sace sadakin da wani barawo yayi,
Jama’a da suka halarci sallar Juma’a a ranar 29 ga watan Janairun 2021 a masallacin Al Noor da ke Abuja sun sha matukar mamaki.
Lamarin mai cike da ban mamaki ya auku ne bayan da aka daura auren wata amarya kuma aka damka kudin sadakinta N100,000 ga waliyyinta amma suka yi batan dabo.
Tuni kuwa waliyyin amaryar ya bayyana batan kudin, lamarin da yasa aka fara caje wadanda ake zargi kuma aka samu kudin a aljihun daya daga cikinsu.
Mutanen da suka yi sallar Juma’ar da ta gabata a masallacin Al Noor da ke Abuja sun sha mamaki
An kama barawon da ya saka hannu a aljihun waliyyin amarya ya kwashe N100,000 na sadaki bayan daurin aure
An damke shi inda ya sha mugun duka, aka tube masa kaya sannan ‘yan sanda suka buga masa ankwa
Jama’a da suka halarci sallar Juma’a a ranar 29 ga watan Janairun 2021 a masallacin Al Noor da ke Abuja sun sha matukar mamaki.
Lamarin mai cike da ban mamaki ya auku ne bayan da aka daura auren wata amarya kuma aka damka kudin sadakinta N100,000 ga waliyyinta amma suka yi batan dabo.
Tuni kuwa waliyyin amaryar ya bayyana batan kudin, lamarin da yasa aka fara caje wadanda ake zargi kuma aka samu kudin a aljihun daya daga cikinsu.
Ganau ba jiyau ba yadda lamarin ya faru ya tabbatarwa da Premium Times yadda aka sanar da daurin auren bayan sallar Juma’a a masallacin Al Noor, inda Sheikh Pantami ke karatu.
Barawon ya gangara zuwa da’irar da masu bada aure da masu karba suke har aka daura. An damka sadakin a hannun waliyyin amarya amma sai ya zura hannu cikin aljihunsa ya sace kudin.
Bayan samun kudin a jikinsa, an yi masa mugun duka sannan aka tube masa kaya kafin daga bisani ‘yan sanda su saka masa ankwa.