Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce an kashe ‘yan fashin da suka tsere a yayin gudanar da samame ta sama a yankin karamar hukumar Giwa wannanna kunshe ne cikin wata sanarwa daga kwamishinan maaikatar tsaron jihar Kaduna Mista Samuel Aruwan, inda ya ci gaba da cewa, “an kara gudanar da wasu ayyuka na musamman a wasu wurare a kananan hukumomin Birnin Gwari, Chikun da Igabi.
Ya ce “Jami’an sojin jiragen sama sun gudanar da bincike a kan Sabon Birni, Rikau, Kaya, Kerawa, Galadimawa, Fatika, Kidandan, Saulawa, Dogon Dawa, Ngede Allah, Kuduru, Yadi, Damari, Takama, Sabuwa, Ungwan Yako, Kaduna-Birnin Gwari hanya, hanyar Ungwan Yako-Kuduru da kewaye.
“Bisa ga bayanin aiki ga Gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar, an ga ‘yan fashi da makami dauke da shanun sata kusan kilomita 3 Kudu maso Yamma na Galadimawa, da alama sun tsere daga yankin saboda harin sama. Sun kasance cikin hanzari, sannan kuma babu komai a tare da su.

“Jami’an sojin sama sun ci gaba da bibiyarsu ta hanyar wata na’urar rediyo tare da sojojin kasa, kuma duk sauran wuraren an rufe sannan an bayar da rahotonsu inda suke da inda suka nufa ba tare da lura da abubuwan da ake zargi ba.” Sanarwar ta ce “A wani aikin na daban, jami’an dake aiki i da jiragen sama sun hanzarta shirya wani aiki a kan kauyukan Kidandan bayan samun rahotannin ayyukan ‘yan fashi a yankin.
“Ko da yake an da cewa lura wurin bai zama mai kyau ba saboda rashin kyan yanayi na gani da babu sosai a yankin a lokacin, amma ma’aikatan sun ci gaba da kasancewa a kan wurin don hana abin kafin su dawo sansaninsu.

“Gwamna Nasir El-Rufai ya lura da rahoton tare da godiya, inda ya yaba wa ma’aikata da sojoji kan kokarin da suka yi na ci gaba,” kamar yadda sanarwar ta kara
A cewar Mista Aruwan, “Masu sintiri na nan za su ci gaba tare da kasancewa cikin shiri a wadannan da sauran bangarorin da ke a duk fadin jihar.”

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *