Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Kungiyar MSS din tsofaffin daliban GSS, Otukpo ta bi ba’asin yunkurin rushe masallaci a harabar makantar

Kungiyar wadda bata dade da kamalla gyara masallacin ba ta ce a dakata da yunkurin rushe masallacin mai shekara fiye da 40

Gwamnatin Jihar Benue ta bakin ma’aikatar ilimi ta ce tuni aka shawo kan wannan batu

Kungiyar dalibai musulmi (MSS) na tsofaffin daliban Government Secondary School (GSS), Otukpo, Jihar Benue, sun bi ba’asin yunkurin rushe wani masallaci da ke harabar makarantar, Daily Trust ta ruwaito.

Amma, gwamnatin jihar ta bakin ma’aikatar ilimi ranar Talata, tayi ikirarin an shawo kan wannan batu.

DUBA WANNAN: Da dumi-dumi: Buhari ya naɗa Aghughu a matsayin sabon AGF

A wata takarda da aka aike wa Kwamishinan ilimi na jihar, Prof. Dennis Ityavyar, kungiyar ta ce hukumar tsare birane da ci gaba (UDB) ranar 20 ga Janairu, 2021, tayi wa masallacin wanda ita (MSS) ba ta dade da gyara shi ba za a rushe.

Yan kungiyar MSS kuma tsofaffin daliban GSS, Otukpo, mun yi rubuta don jin ba’asin rushe masallacin makaranta.

“Muna kira ga kwamishina da a dakata da yunkurin karkata ba mu dade da yi masa kwaskwarima ba a GSS, Otukpo, a kuma dawo da shugaban makarantar saboda idan ka cire wa yarje mana da aka yi don gyara masallacin, ba a ba shi ko kobo ko an tuntube shi don bashi kwangila ba,” kamar yadda kungiyar ta shaida

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *