Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umarnin kwace kudaden bankunan Abdulaziz Yari

Kotun ta bada wannan umarnin ne sakamakon maka tsohon gwamnan kotu da hukumar ICPC tayi

Alkalin kotun ya ce bai ga dalilin da zai hana hukumar ICPC kwace kudaden bankunan tsohon gwamnan ba

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya sanar da yadda wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umarnin kwace kudaden da ke bankuna na tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari.

Kudaden sun hada da wadanda ke bankunan Zenith da Polaris na kasar Najeriya, BBC Hausa ta wallafa.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran ya ruwaito, kudaden da ke bankin Polaris sun kai dala hamsin da shida.

Akwai Naira miliyan 12.9, Naira miliyan 11.2, dala 30,309.99, Naira 217,388.04, dala 311,872.5 wadanda aka adana a bankin Zenith duk da sunan tsohon gwamnan da kamfanoninsa.

Kamar yadda alkalin kotun ya yanke, ya ce babu dalilin da zai sa hukumar ICPC wacce ta shigar da karar ta kasa kwace kudaden.

Idan za mu tuna, hukumar ICPC tana zargin tsohon gwamna Abdulaziz yari da samun makuden kudaden ta haramtacciyar hanya.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *