Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfes Attahiru Jega, ya bayyana gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a matsayin ”babban abin takici.”
Yayin wata tattaunawa da jaridar Daily Trust, Jega ya ce gwamnatin Buhari ”ta gaza fitar da yawancin ‘yan Nigeria kunya”, kamar yadda TheCable ta wallafa.
Farfesa Jega ya rike hukumar INEC daga shekarar 2010 zuwa 2015, shekarar da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya sha kaye a hannun Buhari.
Tsohon shugaban kungiyar ASUU da Jami’ar BUK da ke Kano, Farfesa Jega ya kasance shugaban INEC na farko, kuma daya tilo har yanzu, da ya fara gudanar da manyan zabuka guda; a 2011 da 2015.
A cewar Farfesa Jega, duk da har yanzu ‘yan Nigeria na yi wa Buhari fatan alheri, ‘yan kasa suna cikin damuwa ”akan alkiblar da kasa ke dauka.”
“Buhari ya bawa mutane da yawa mamaki. Har yanzu yana da lokacin gyara al’amura idan zai iya hakan. Amma, maganar gaskiya, gwamnatin ta kasance babban abin takaici,” kamar yadda Jega ya bayyana.
“An samu tabarbarewa al’amuran gwamnati a matakin tarayya da mafi yawan jihohi, hakan ne kuma yasa mu ke fama da kalubale a ko ina; yakin Boko Haram, ‘yan bindiga, fashi da makami, da sauransu,” a cewarsa.
Kalaman Farfesa Jega sun shiga sahun na saura manyan kasa irinsu tsohon shugaba Olusegun Obasanjo da Farfesa Wole Soyinka, wadanda suka dade da fara sukar gwamnatin Buhari.