Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Cutar Coronavirus na ci gaba da yaduwa a Jihar Kano inji Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano

Gwamnan ya bayyana takaicin sa kan yadda mutane ke kauracewa matakan kariya duk da yadda cutar ke yi wa jihar barazana

An bayyana cewa cikin kwanaki 49 da suka gabata, an samu yawaitar masu cutar yayin da 17 suka mutu

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a ranar Laraba ya bayyana cewa annobar COVID-19 ta dawo a jihar ta shi, tare da yin kamari fiye da karon farko an annobar, The Nation ta ruwaito.

Ya ce mutane 17 cutar ta kashe cikin kwanaki 49 da suka wuce, yayin da yiwuwar kama cutar ya karu zuwa kaso 12.7, in aka kwatanta da 4.2 na baya

A gaba daya, zuwa ranar 18 ga watan Janairu, cutar ta kashe mutane 71, ta kama mutane 2,636 daga cikin 61,802 da aka gwada da kuma 61,997 da aka zargi su na da cutar.

Majinyatan da ke gida da asibiti ya kai 289 cikin kwanaki 49 da suka gabata.

An ruwaito cewa an sallami mutane 2,276 kuma ana neman mutane 5,083 da suka yi mu’amala da masu cutar.

Inda aka fi samun yawan masu kamuwa da COVID-19, kamar yadda gwamnatin jihar ta ce, karamar hukumar Nasarawa, 624, sai Tarauni, 499 da kuma Kano Municipal mai 286.

Ganduje ya ce yana bakin cikin yadda mutane ke kauracewa matakan kariya duk da yadda cutar ke barazana a jihar.

Karin wasu matsalolin da Ganduje ya fada, sun hada da “rashin yadda da cutar gaba daya (da yawa ba su yadda COVID-19 gaskiya ba ce), rashin bada hadin kai ga wanda aka tabbatar yana dauke da cutar wajen killace kansu ko su bari a kai su wuraren da aka tanada”.

Wakilin mu na fadar Gwamnati Kasim Gambo Kasim ya ruwaito cewa abu ne mai wahala a tilasta bin dokokin a jihar.

Dr Sabitu Shu’aibu Shanono, mataimakin shugaban kwamitin dakile COVID-19 a Jihar Kano, ya ce “mutane 17 ne suka rasu daga watan Disamba zuwa Janairu sanadiyar cutar a jihar.”

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *