Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta jihar kano Sharu Rabiu Ahlan yace hukumarsa bazata lamunci yadda wasu yan kungiyoyi a rukuni na daya dana biyu da aka fara gasarsu ke yin amfani da wasu manyan yan wasa da aka cimma yarjejeniyar kin amfanin dasuba,

A wata tattaunawa ta wayar salula da yayi cikin shirin labarin wasanni na Express Radio Sharu yaja kunnen kungiyoyin dake amfani da yan wasan da suka buga a wasannin ajin matasa na kasa wato Nationwide dasu dena ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani,

Sharu Ahlan Wanda kuma shine shugaban kwamitin alkalancin wasan kwallon kafa na kasa yace kananan rukuni na jihar kano a tanadesu ne dan matasan yan wasa da suke tasowa saboda haka babu wani dalili da zaisa wani dan wasa ya shekara 10 yana baga Nationwide league yazo ya tarewa matasa guri ” Bazamu yarda ba” inji Ahlan,inda yace a halin yanzu hukumar ta Nada wasu wakilai na sirri da zasu dinga zuwa filayen wasan suna kula da manya yan wasa kuma hukumar ta sa a dinga dauka hoto dan kafa sheda,

Dayake amsa tambaya kan ko an taba kawo karar wasu kan wannan batun cewa yayi ai babu maganar kawo kara hukumace taga dacewar ta takawa abin birki saboda haka ba sai an kawo kara ba, hukuma zata bibiyi kungiyoyi duk Wanda ta samu da laifin sanya irin wadanna yan wasa to zatayi hukunci ko an kawo kara ko ba a kawo ba, dan tabbatar da adalci da cigaban wasan a jihar kano, kuma zamu tabbatar babu wata dama da za a bayar dan yin almundahana,

Daga nan sai shugaban hukumar kwallon kafar ta jihar kano ya jin jinawa Yan kwamitin kula da gasar bisa irin jajircewarsu na ganin gasar ta tafi yadda ya kamata,inda yace matasan dake kwamitin kula da gasar zasu zama abin alfahari ga jihar kano saboda yadda suke gudanar da aikin su cikin gaskiya da rikon amana,

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *