Yau Donald Trump zai bar mulkin kasar Amurka ba don yana so ba
Za a rantsar da Joe Biden a matsayin sabon Shugaban kasar Amurka
Trump zai yi wa wasu mutane afuwa kafin ya sauka daga kan kujera
Shugaban kasar Amurka mai barin-gado, Donald Trump, ya yi kwanansa na karshe a fadar White House a ranar Talata, 19 ga watan Junairu, 2021.
Jaridar Punch tace mako guda kenan aka shafe ba tare da an ga Donald Trump a fili ba, tun da aka dakatar da shugaban kasar daga Twitter, ya yi tsit.
Haka zalika har yanzu Trump bai taya Joe Biden murnar lashe zaben da aka yi ba, ko ya gayyace shi zuwa fadar shugaban kasa ko ya masa barka.
Daga cikin ayyukan da shugaban mai barin-gado zai yi karshe shi ne, zai ziyarci garin Florida a yau Laraba, inda zai yi wa wasu masu laifi afuwa.