Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Dan gwamnan jihar Kaduna, Bashir El-Rufai ya sha caccaka tare da barazana bayan wallafa hoton mahaifinsa da na Tinubu

Bashir ya wallafa hoton ne tare da tsokacin cewa wannan muhimmiyar hadaka ce Najeriya ke bukata, lamarin da ya janyo cece-kuce

– Wani matashi yace sai ya yi wa Bashir duka a cikin cacar bakin amma Bashir ya tabbatar da cewa harsasai 1000 za su isa garesa da tsatsonsa kafin ya kusanto shi

Bashir El-Rufai, daya daga cikin yara mazan gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai ya yi wallafar da ta tada kura a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

Da rikicin tare da cacar bakin ta tsananta, Bashir ya ja kunnen wani matashi da yayi barzanar kai masa hari matukar sun hadu.

Lamarin ya fara ne bayan Bashir ya wallafa hoton mahaifinsa da jigon jam’iyyar APC, Bola Tinubu inda yace “Kudu maso yamma da arewa maso yamma. Muhimmiyar hadakar da Najeriya za ta amfana da ita.”

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *