Gwamnatin Jihar Kaduna tace KADPOLY da Open University kadai ne za a bude
Za a cigaba da rufe duka sauran makarantu har da A.B,U Zaria saboda COVID-19
Ana sa ran a bude makarantu a Najeriya a ranar Litinin, 18 ga watan Junairu, 2021, bayan tsawon lokacin da aka dauka a gida saboda annobar COVID-19.
Amma a jihar Kaduna, gwamnatin Nasir El-Rufai ta ce za a cigaba da rufe duk wasu makarantun da ke jihar, har da manyan makarantun gwamnatin tarayya.
Jaridar Daily Trust tace Sakatariyar din-din-din ta ma’aikatar ilmi na jihar Kaduna, Phoebe Sukai Yayi, ta bada wannan sanarwa a ranar Lahadi, 17 ga watan Junairu.
Phoebe Sukai Yayi ta bayyana cewa suna lura da yadda cutar COVID-19 ta ke cigaba da yaduwa a Kaduna.