Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Sama da motocin dakon kaya goma cike da sojoji da ‘yan sanda ne suka wuce ‘yan jarida da aka shinge su ‘yan mitoci kalilan daga gidan Kyagulanyi Sentamu, da aka fi sani Bobi Wine. Wasu sojoji kalilan kuma suna sintiri da sawu a kusa da gidan.

Hukumomi sun hana jama’a har da ‘yan jarida kaiwa ga gidan madugun ‘yan adawan Robert Kyagulanyi, wato Bobi Wine, babu mai shiga kuma ba mai fita gidan.

Dan majalisa Francis Zaake mai goyon bayan Wine da aka taba kama shi a baya kana ake zargin jami’an tsaro sun azabtar da shi, shine kadai mutumin da aka bashi damar kaiga shinge da aka tsare hanya dashi. Sa’annan daga bisani aka fito da shi a cikin motar sa aka lakada masa dan karen kashi kana aka jefa shi cikin motar ‘yan sanda. An dai tsare ‘yan jarida daga nesa, kana yayin da motar ‘yan sandan ke shigewa an ji Zaake yana ihu cikin motar.

Shugaban hukumar zaben Simon Byabakama, ya bada sanarwar sakamakon zaben ne bayan karfe hudu na yamma agogon kasar, inda ya ce Yoweri Museveni ne ya lashe zaben a karo na shida a wa’adin shekaru biyar a matsayin shugaban kasa.

Jami’ai sun ce shugaba Museveni ya lashe kashi 58.64 cikin dari na kuru’un, yayin da Wine ya samu kashi 34.83 cikin dari na kurun da aka kada a ranar Alhamis.

Byabakama ya yi kira al’ummar Uganda musamman magoya bayan dan takarar da ya sha kashi da su gujewa tada rikici.

Shugabannin ‘yan adawa sun ki amincewa da sakamakon, suna cewa ba zasu zauna su nade hannun su ba, saboda sakamakon ba na gaskiya bane. A ranar zaben, sama da masu sa ido kan zabe 30 ne aka kama.

Ofishin jakadancin Amurka a Uganda yaki yin aikin sa ido a kan zabe, bayan da hukumomi suka hana sama da kashi 75 cikin dari na bukatar da ya shigar na neman takardun izini aikin sa idon.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *