An sami karin mutane 1,270 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, jimilla 102,601.
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin jakadu 95 zuwa kasashe daban-daban.
An yanke wa sojan da ya kashe soja hukuncin kisa ta hanyar bindigewa.
Shugaban ‘yan sandan Najeriya ya sauya wa wasu manyan jami’an ‘yan sanda wuraren aiki.
Jami’ar Ahmadu Bello Zaria za ta buɗe makaranta a ranar 25 ga watan Janairu 2021.
Mutane 38 sun rasa rayukansu sakamakon guguwa da zubar dusar kankara a Japan.
Kasar Iran ta caccaki Amurka kan kungiyar AlQa’idah.
Chelsea na shirin mayar da tsohon kocinta Avram Grant.
Real Madrid za ta sayar da ‘yan wasanta 6 domin ta iya dauko Mbappe.
EPL: Manchester United ta sami nasara a kan Burnley da ci 1:0 a wasan jiya.
EPL: Everton ta sami nasara a kan Wolverhampton da ci 2:1 a wasan jiya.
LaLiga: Athletico Madrid ta sami nasara a kan Sevilla da ci 2:0 a wasan jiya.