Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wani dan majalisa, mai wakiltar Bodinga-Dange, a mazabar tarayya ta Shuni-Tureta, Dr. Balarabe Kakale ya ware naira miliyan 200 domin karfafawa Almajiri da kananan ‘yan kasuwa a mazabar sa, Daily Trust ta ruwaito.

A wata hira da aka yi da shi jim kadan bayan rarraba motoci tara, babura 33, kekunan dinki 60, injunan nika 40 da sauransu ga wadanda suka fara cin gajiyar shirin, ya ce an yi hakan ne domin a hana Almajirai yin bara.

Ya kara da cewa yana harin tallafawa almajirai 1000 ne a wannan shekarar kadai, ya kara da cewa shirin zai ci gaba ne.

A cewarsa, an kuma samar da kudin ne don karfafa Makarantun Allo (makarantun Alkur’ani) da Malaman su

Wannan shine dalilin da ya sa muka rarraba kananan motoci guda 4 zuwa Makarantun Allo da babura 33 ga Malamansu, wadanda za su iya amfani da su wajen samar da kudin shiga.

“Kuma mun bai wa masu karatun Makarantun Allo, mata da mutane masu fama da nakasa da sauran ‘yan kasuwa karfin gwiwa da kayayyakin aiki da kuma rancen da ba ruwa,” in ji shi.

Ya bayyana cewa an yiwa aikin lakabin “Kowa Ya Iya Allon shi, sai shi wanke,” saboda an yi shi ne don sanya Almajirai su dogara da kansu.

Kakale wanda ake kira da suna “Memba mai Allo” don yin gwagwarmayar tabbatar da Almajiri a kasar, ya kara da cewa an kafa kwamiti da zai bibiyi ayyukansu tare da tabbatar da cikakken dawo da bashin.

“Saboda abokan huldarmu na banki sun yi alkawarin bayar da kudin da ya dace, idan aka samu nasarar kwato kudaden,” in ji shi.

Kakale wanda ya kasance mai daukar nauyin dokar sauya fasalin almajiranci a karamar majalisar, ya nuna adawa ga tsarin almajiranci saboda tsarin karatunsu ba ya karfafa kwazo.

Ya kuma lura cewa gwamnatin tarayya na shirin fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci, ba zai yi nasara ba, ba tare da damawa Almajirai ba.

Ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari, Ministocin Harkokin Jin Kai, Harkokin Mata da gwamnatin jihar Sakkwato kan yadda suka nuna damuwa kan halin da Almajirai ke ciki a kasar.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *