Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Sabanin yadda wasu kungiyoyi da ake zaton na bogine ke shirya atisaye daban daban da zimmar tantance yan wasan kwallon kafa tare da karbe musu kudade su tsere,

Kungiyat ATM Sports da ta shirya tamtance yan wasa a jihar kano ta bakin shugaban kungiyar Jamyl MD Abubakar yace kungiyar su bata bukatar ko kwabo daga wani dan wasa ko wata kungiya don daukar dan wasa,

Jamilu MD yace lokaci yayi da za’a gane irin wadanda ke amfani da irin wannan dama suna damfarar alumma da yan wasan da Idonsu ya rufe,
” Mu bama bukatar kudin kowa kuma bama umartar abawa ko kudi dan shiga shirin mu ” inji Jamyl Md Abubakar dake matsayin shugaban kungiyar dake shirin tantancewa da zabin yan wasa a jihar kano

Dan gane da yadda fitowar yan wasa wajen tantancewar Jamyl MD cewa yayi akwai ban mamaki yadda matasa yan kwallon suka fito kuma suke baje irin basirar da suke da ita abin dake nuni da ce lallai akwai matasan yan wasa a arewacin Najeriya dake bukatar taimakon irin kugiyoyin mu dan bunkasa cigaban su,

Dan gane da yadda kungiyar ATM Sports Academy tasa gaba Jamyl MD cewa yayi bamu da wani buri Illa muga mun bawa mara karfi ko Gata wata dama da zai zama wani a cikin rayuwa, ” Munfi so dan talaka mara gata ya zama abin alfaharin alumma saboda basirar da Allah ya bashi ” inji Shugaban kungiyar ATM

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *