Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Labaran Yammacin Lahadi 10/01/2021CE – 26/05/1442AH. Kanun labarai

Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Bala Ngilari, ya ce PDP ba za ta iya yi wa Najeriya wani kokari fiye da APC ba.

Kungiyar Amotekun ta kai wa fulani hari tare da kashe wani mutum da ‘ya’yansa biyu a jihar Oyo.

Sojoji a jihar Zamfara sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga 50 da kwato dabbobi sama da 300.

‘Yan bindiga a ranar Asabar sun kai hari wani kamfanin shinkafa da ke jihar Kano.

Gwamnatin Kaduna ta musanta rahoton cewa jirgi na kaiwa ‘yan bindiga makamai.

Gobara ta ƙone ofisoshi a hukumar kula da shige da fice ta Najeriya da ke Abuja.

Fiye da mutum 4000 ne suka kamu da korona a Amurka rana guda.

Zaizayewar ƙasa ta kashe mutum 11 a Indonesia.

Jami’an tsaron Mali na neman tsohon fira ministan kasar, Boubou Cisse ruwa a jallo.

Spain na fuskantar zubar dusar kankara mafi tsanani cikin shekaru 50.

Man United ta fasa sayen dan wasan Ecuador mai shekara 19, Moises Caicedo.

FA Cup: Chelsea ta sami nasara a kan Morecambe da 4:0 a wasan yau.

FA Cup: Manchester City ta sami nasara a kan Birmingham City da ci 3:0 a wasan yau.

Seria A: Roma da Inter Milan sun tashi 2:2 a wasan yau.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *