An sami karin mutane 1,585 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, jimilla 99,063.
Hukumar NDLEA ta ce ta dakatar da daukar sababbin ma’aikatanta ne saboda annobar Covid-19.
Gwamna Ganduje na jihar Kano ya kai ziyarar ta’aziyya ga Sanata Kwankwaso.
Hatsarin mota tsakanin Motar sojoji da wasu ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5 a jihar Kwara.
Hukumar ‘yan sanda ta bullo da wani sabon manhaja da za ta rika amfani da shi don gano masu aikata laifi.
Hukumar FRSC ta ce dole sai mutum ya mallaki katin dan kasa sannan za a sabunta masa lasisin tuki.
Covid-19: Gwamantin jihar Delta ta bayar da umurnin sake bude makarantu a ranar 18 ga watan Janairu 2021.
Ministan Sadarwa ya ce ana da damar hada layukan waya 7 a katin zama dan kasa daya.
Jarirai 10 suka rasu a wata mammunar gobara a wani asibitin Indiya.
Turkiyya ta ce a shirye take ta gyara hulda da Faransa.
Dusar kankara ta yi sanadiyar rayuwar jariri a Siberia da ke kasar Rasha.
FA Cup: Arsenal ta sami nasara a kan Newcastle United da ci 2:0 a wasan jiya.
FA Cup: Manchester United ta sami nasara a kan Watford da ci 1:0 a wasan jiya.
LaLiga: Barcelona ta sami nasara a kan Granada da ci 4:0 a wasan jiya.