Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta cafke wasu mutum 4 da ake zargi da hannu a mutuwar wata budurwa mai shekaru 18 a masaukin bakin gwamnatin jihar Yobe da ke Damaturu.
Premium Times ta gano cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis. ‘Yan sandan sun damke mutanen da ake zargi da hannu.
Majiya daga rundunar ‘yan sandan ta ce babban wanda ake zargin shine wani mutum mai suna Al-bash Yahaya Ibrahim tare da wasu mutum uku.
An mika gawar matashiyar asibitin kwararru na jihar Yobe da ke Damaturu domin gano abinda ya kasheta.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
“An kama mutum hudu da ake zargi da kisan kai,” yace.
Kamar yadda yace, “Dukkan abubuwan da ake zarginsu da shi za su bayyana ne bayan an gano musababin mutuwar yarinyar.”
“Wani Dr Al-Bash Ibrahim Yahaya ya sanar da ‘yan sanda cewa ya kwana da matashiyar kuma ta rasu a dakinsa.
“Ya sanar da ‘yan sanda cewa shi bako ne a gidan gwamnatin jihar Yobe kuma ya bukaci da a kawo mishi matashiya wacce za ta taya shi kwana. Ya kwana da ita amma sai da safe ya gane cewa a bige take.
“Ya ce ta fara wasu abubuwa tare da kakkarwa. Binciken farko ya nuna a bige take da kwayoyi,” Dungus yace.