An sami karin mutane 1,544 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, jimilla 97,478.
Shugaba Buhari ya ce za a kawo karshen Boko Haram a wannan shekarar.
Najeriya za ta ginawa ‘yan gudun hijira gidaje 600 a Maiduguri.
Gwamnatin jihar Kaduna ta karyata jita-jitar wani jirgi ya sauke wasu ‘yan ta’adda a Zaria.
Boko Haram sun kashe mutum 3, sun yi awon gaba da dabbobi a kusa da Maiduguri.
Shugaba Trump na Amurka ya ce ba zai halarci bikin mika mulki ba a ranar 20 ga Janairu.
Iran ta haramta shigar da riga-kafin korona da aka yi a Amurka da Ingila ƙasarta.
An sace komfutar shugabar majalisar dokokin Amurka Nancy Pelosi a hargitsin Capitol Hill.
An saka dokar hana fita waje a Jamhoriyar Afirka ta Tsakiya.
Messi ya zabi komawa PSG don hadewa da Neymar.
FA Cup: Liverpool ta sami nasara a kan Aston Villa da ci 4:1 a wasan jiya.
FA Cup: Wolverhampton ta sami nasara a kan Crystal Palace da ci 1:0 a wasan jiya.
Bundesliga: Borussia Moenchengladbach ta sami nasara a kan Bayern Munich da ci 3:2 a wasan jiya.