Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Tsohon dan majalisar jiha kuma dan takarar shugabancin karamar hukumar Tarauni Abubakar Zakari Habu P.A ya sha alwashin bunkasa harkokin matasa dac wasanni da zaran ya dare kujerar mulki a karamar hukumar,

Habu P.A na wannan bayani ne gabanin fara wata katafariyar gasa irinta ta farko da aka sanya mai taken HABU P.A 2021 CUP wadda fittaccen mai horar da kungiyar karkasara united Coach Danbala Ziba zai jagoranta.

Bai zama bakon abuba irin gudummawar da tsohon dan majalisar ya bayarba lokacin yana majalisa, ko iyanzuba duba da irin rawar da ya taka na samarwa matasa kyakykyawan yanayi motsa jiki da bunkasa harkokin wasanni,

Matashi Habu P.A zai zama tauraro wajen haska irin basirar da matasa ke da ita musamma karamar hukumar Tarauni wacce take da dinbin matasa masu basirar taka Leda

Hakanne ya sanya matasan yankin shirya gasar da zaayi amfani da ita wajen sauya fasalin yadda zaa dora matasan kan gwadabe me dorewa da samun cigaba,

Jagoran shirya gasar Danbala Ziba ya kara da cewa tunba yanzu ba Habu P.A keda shaawar tallafawa matasa a harkokin wasanni abin da Ziban ke cewa zuwa kusa da matasan yanzu zai baiwa P.A damar cika burin dayake dashi lokacin wadancan mukaman daya rike,

A safiyar . ranar lahadi ne za’a bude gasar da ake sa ran halartar dantakarar da manya manyan shugabannin yankin,a filin wasa na asibitin koyar wa na Malam Aminu Kano

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *