Yan wasan Kungiyar kwallon kafa ta Jido Warriors dake garin Jido a yankin karamar hukumar Dawakin Kudu sun sha alwashin fidda Mara kunya a wasan karshe da zasu fafata na gasar cin kofin kano central,
A wata tattaunawa da express radio tayi da wasu yan wasan kungiyar a wani wasan sada zumunta da kungiyar ta shirya a garin Jido da taya murna samun karuwar ya’ya 3 da shugaban kungiyar Auwalu Jido A.A Jido ya samu yan wasan sunce suna sane da kalu balen dake gabansu na wasan karshen amma lokaci yayi da suma zasu cikawa magoya bayansu da alummar Jido da Dawakin Kudu irin alkawarin da sukayi na ganin sun sami nasara,
Wani daga cikin yan wasan wanda baiso fadin sunansa ba dake bugawa a tsakiya yace tunanin su a kullum shine sukai wasan karshe a kowace gasa ba kawai gasar kano central ba, saboda haka ya zama wajibi a garemu mu jajirce dan ganin mun baiwa Mara da kunya,
Da suke bayani kan sirrin samun nasarar kungiyar yan wasan cewa sukayi cikkaken goyon bayan da suke samu daga alummar garin Jido manya da yara, maza da mata musamman Uban kasar Jido wato Dagaci Wanda da bazarsa kungiyar da matasan yankin ke rawa kana suka bayyana kishi halin kan yan wasa da kaunar juna a matsayin manyan sirrikan samun nasarar kungiyar,
Wani bincike da express radio ta gudanar kan yan wasan dake bugawa a kungiyar ya nuna cewa kaso Dari bisa Dari duk yan Garin Jido ne sabannin yadda wasu kungiyoyi a wasu garuruwa ke dauko yan wasa daga wasu gurare dan buga musu wasa,
Da yake karin haske kan irin wannan dama da yan asalin Jido suka samu sabanin sauran garuruwa shugaban kungiyar A.A Jido cewa yayi Allah ya albarkaci gsrin da dinbin matasa masu basira a fagen wasan kwallon kafa kuma musu son suyi wasan to ” Me zai samu zuwa waje dauko sojan haya” amma fa ba ina nufin mun iyakance cewa sai dan garinmune zai bugawa kungiyar ba a’a kowa ma zai iya zuwa matukar yana da shaawa kuma daga ko ina inji A.A Jido,
Abin alfahari ga kungiyar shine yadda a lokaci guda karanta ke Neman kaiwa tsaiko tsakanin takwarorinta a jihar kano duba da nasarorin data samu a wasa Barau kano central Wanda ya bata damar kaiwa wasan karshe na cin kofin wasan da ake saran zata fafata da kungiyar Ganduje Academical wata kungiya da itama tayi fice a gasar,
Dan gane da kungiyar da zata buga wasan karshe da ita ya wasan na Jido cewa sukayi kullum a shirye muke da kowace irin kungiyar a koda yaushe kuma a ko ina saboda haka bama shakkar zamu samu nasara a wasan da ikon Allah.