An sami karin mutane 917 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, jimilla 90,080.
Gwamna Wike na jihar Rivers ya bayar da umurnin sake bude makarantu a jihar a yau Litinin.
2023: Sanata Ibrahim Shekarau ya ce babu tsarin karba-karba a cikin jam’iyyar APC.
COVID-19: Gwamnatin Najeriya ta haramta wa mutum 100 fita kasashen waje saboda kin gwaji.
‘Yan sanda sun cafke mutane 18 da ake zargi da tada tarzoma a Zamfara a jiya Lahadi.
Sheikh Ahmad Gumi ya ziyarci wasu garuruwa da suka yi kaurin suna wajen sace-sacen mutane a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
‘Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 3 a yayin da aka yi garkuwa da wani likita a jihar Oyo.
Garba Shehu ya ce ‘yan Najeriya ba za su lamunta da dawowar PDP a 2023 ba, domin sun san jam’iyyar da karya.
Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan mutane 70 a Jamhuriyyar Nijar.
An yi garkuwa da ma’aikatan mahakar kwalli a Pakistan.
EPL: Manchester City ta sami nasara a kan Chelsea da ci 3:1 a wasan jiya.
EPL: Leicester City ta sami nasara a kan Newcastle United da ci 2:1 a wasan jiya.
LaLiga: Barcelona ta sami nasara a kan Huesca da ci 1:0 a wasan jiya.
LaLiga: Atletico Madrid ta sami nasara a kan Alaves da ci 2:1 a wasan jiya.