Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Dattijo, Alhaji Tanko Yakasai, ya yi tsokaci ga tsarin mulkin karba-karba na shiyya-shiyya akan waɗanda suka cancanci su karɓi mulkin kasar nan a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.

A cewar Yakasai, ƙabilar Igbo ba zasu samu mulkin kasar nan ba har sai sun zage damtse, ya ƙara da cewa, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ma ya cire maitarsa ta son sai ya yi mulki a 2023.

Ya ce, tsarin mulkin ƙasar nan ne kaɗai zai bayyana wanda zai karɓi mulki ba tsarin karɓa-karɓa ba wanda bai da tushe cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya ba.

A cewar dattijo Yakasai, banbancen da ke tsakanin al’ummar arewa ya yi yawan da ba zai barsu su yi magana da murya daya ba, a saboda haka Tinubu ya daina saka ran cewa zai samu goyon bayan ‘yan arewa kamar yadda ya ke tsammani.

Yakasai ya kara da cewa Jama’ar arewa da ‘yan Nigeria da dama ba zasu goyi bayan Tinubu ba saboda rawar da ya taka wajen kawo mulkin Buhari.

Ba’a taɓa bayar da mulki a banza ba, tsarin zaɓe ne ke bayarwa. Ina son yan kudu maso gabashin ƙasar nan da su samar da ɗan takarar mai inganci saboda kudu maso yamma sun samar da irinsa; wato Obasanjo.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *