Majalisar koli ta addinin musulunci ta yaba wa Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna kan rusa gidan casu a jihar.
Hukumar EFCC ta kama mutum 21 da zargin zamba ta intanet.
Gwamnatin jihar Ebonyi ta bayar da umurnin sake bude makarantu a jihar ranar 18 ga watan Janairu 2021.
Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna ya yi wa ‘yan gidan yari 12 afuwa.
‘Yan sadan Zamfara sun daƙile harin ‘yan fashin daji.
Wata mota da ta maƙale a cunkoson ababen hawa ta fashe a arewa maso gabashin Syria.
Hukumar zaɓen Nijar, CENI ta tabbatar da cewa za a je zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasar Jamhuriyar Nijar.
Ministan harkokin wajen China, Wang Yi, ya yi ikirarin cewa ba wai a ƙasar kaɗai cutar corona ta samo asali ba.
Kasar Brazil ta janye wa talakawa tallafin annobar Coronavirus na wata-wata.
PSG ta dauki tsohon kocin Tottenham da Southampton, Mauricio Pochettino a matsayin sabon kocinta.
EPL: Tottenham ta sami nasara a kan Leeds United da ci 3:0 a wasan yau.
LaLiga: Villarreal ta sami nasara a kan Levante da ci 2:1 a wasan yau.