An sami karin mutane 1,031 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, jimilla 87,510.
Jami’an ‘yan sanda sun kama mamallakin jaridar Sahara Reporters, Sowore a Abuja.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta damke wani soja mai mukamin Kofur da laifin kisan mahaifiyarsa.
Mayakan Boko Haram sun sace mata 4 a Adamawa.
2020: Hedikwatar tsaro ta kasa ta ce a cikin shekarar dakaru sun kashe ‘yan ta’adda 2,403.
Wani dan acaba ya mutu bayan da jami’an Kwastom suka buge shi a mota a yayin da suke bin wata mota da aka yi sumogal din shinkafa a Ogun.
Fitaccen lauyan nan, Femi Falana ya ce talauci ya fi Covid-19 kisa a Najeriya.
Ofishin Kula da Bashin ya ce bashin Najeriya ya tashi zuwa Naira trilyan 32.223.
Najeriya ta yi Allah-Wadai da harbe dan kasarta a Ireland.
Majalisar Dinkin Duniya ta kawo karshen zaman sojojinta a yankin Darfur.
Fararen hula 28 ne suka rasa rayukansu, wasu 13 kuma suka jikkata sakamakon harin da aka kai wa wata mota a Siriya.