Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Bishop Kukah ya shawarci kafofin watsa labarai da su kawo rahoton labari yadda yake ba tare da kowani murdiya ba

Kukah na martani ne ga sukar da ake masa kan sakonsa na Kirsimeti zuwa ga yan Najeriya

Bishop ya bayyana cewa ra’ayin kansa kawai ya fada

Daga karshe Bishop na Katolika da ke Sokoto, Mathew Hassan Kukah, ya fayyace biri har wutsiya kan cece-kucen da sakonsa na Kirsimeti ya haifar.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa babban faston ya ce shi bai yi kira ga juyin mulki ba a sukar da yayi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kamar yadda aka rahoto, cewa kawai dai ya fadi ra’ayinsa ne bisa hujja.

Legit.ng ta tattaro cewa yayinda ya ke zargin Buhari da son kai a sakonsa na Kirsimeti a ranar Juma’a, 25 ga watan Disamba, faston ya ce idan da ace Musulmin da ba dan arewa bane ya aikata abunda Buhari ya aikata, toh da an yi masa juyin mulki.

Da yake zantawa da manema labarai a daren ranar Litinin, 28 ga watan Disamba, Kukah ya ce babu adalci a rahoton cewa shi ya nemi ayi juyin mulki.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *