Aƙalla shaguna 252 ne wuta ya lalata a gobarar da ta faru a kasuwar Galadima da ke Gwarimpa a Abuja.
2023: Gwamnan Badaru na jihar Jigawa ya ce ba shi da asarar komai idan APC ta sha kayi a jiharsa.
‘Yan majalisar wakilai sun ce ba su nemi afuwar Buhari ba don sun gayyace shi, ya ki zuwa.
Gwamna Sule na jihar Nasarawa ya ce ba jiya ce ta kai shi Amurka ba, ya je shakatawarsa ne.
Gwamnatin jihar Lagos ta ce ta gano masu sayan takardun shaidar gwajin Covid-19 na bogi.
Wasu mafusata sun cinna wa wani mai tuka Keken-Napep wuta a Delta bayan ya saci yara biyu.
Ma’aikatar Shari’a ta ƙasar Saudiyya ta haramta aure ko aurar da ƴammata ‘yan ƙasa da shekara 18 da haihuwa.
China ta ɗaure ‘yar jaridar da ta ba da rahoton ɓarkewar annobar korona a Wuhan.
Jami’an tsaro sun kashe masu iƙirarin jihadi 37 a Mozambique.
Eritrea ta girke dakarun tsaro a yankin da ke fama da rikici a iyakar Ethiopia da Sudan.
Guguwar Bella ta katse lantarkin sama da gidaje dubu 40 a Faransa.
Christiana Ronaldo ya lashe kyautar gwarzon dan wasan karni.