Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Hukumar hisbah a garin Yauri da ke jihar Kebbi ta kafa wasu sabbin dokoki ga al’umman jihar a kokarinta na dinke wasu baraka tare da ladabtar da mutanenta.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta kuma wajabtawa limamin da zai daura aure ya tabbatar da an gabatar masa da sakamakon gwaje gwaje da ma’auratan suka yi daga babban asibiti.

Ya kuma haramtawa matasa saka wandon sagin da askin banza.

Abubuwan da Hisbah ta hana aikatawa cikin garin Yauri

“1. Gwaji ga Ma’aurata

“Namiji: Gwajin Kanjamau (HIV/AIDS), gwajin Anta (Hypatitis).

“Macce: Gwajin Kanjamau (HIV/AIDS), gwajin anta (Hypatitis), gwajin ciki.

“2. An hana sa wandon sagin

“3. An hana askin banza

“4. An hana P.E.S.

“5. Ba’a kai karfe 6 na marance wajen talla cikin kasuwa

“6. Ba’a daukan mata biyu a mashin sai da lalura

“7. Ba’a awo da kwanon da ya lankwashe

“8. An hana kide-kiden D.J. Da Wasigidi

“9. An hana buga 9jaBet

“Wajibi ne duk Limamin da zai daura Aure ya tabbatar da an gabatar masa da takardar sakamakon gwaje-gwajen da aka yi daga babban likita na babbar asibiti (General Hospital) kafin a daura aure.

“Wanda duk aka samu ya sabama wannan zai fuskanci sharia

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *