Shugaba Buhari ya rattaba hannu a sabuwar dokar zabe dake nuna duk mataimakin shugaban Kasa ko Gwamna da ya gaji mai gidansa zango daya zaiyi.
Sanata Ali Ndume yayi Allah wadai da hare-haren da Boko Haram suka kai jihohin Adamawa da Borno.
Gwamnatin jihar Legas ta wajabtawa sabbin ma’aurta da sunemi izinin gwamati kafin su shirya shagalin biki a jihar.
Wasu ‘yan bindiga sun sace mai jego a jihar Jigawa.
‘yan bindiga sun kashe mutane 18 da sace 2 a jihar katsina.
Shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan yace dole sai anyiwa kowanne dan Najeriya riga kafin korona.
Kasar Ingila ta nesanta kanta daga zargin Yakubu Gowon daga wawushe baitil malin Najeriya.
Akalla mutane 20 sun mutu sakamakon kifewar jirgin ruwa a Bahar Rum.
Isra’ila takai hare-hare a wurare daban daban a birnin Gaza bayan harba rokoki zuwa cikin kasarta daga can.
EPL: Manchester United da Lecester City sun tashi 2:2 a wasan da suka buga yau.