An sami karin mutane 712 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, jimilla 82,747.
Covid-19: Kungiyar Likitocin Najeriya sun ce a cikin mako guda likitoci 20 suka mutu sakamakon cutar.
2023: Gwamna Badaru na jihar Jigawa ya ce rikicin cikin gida na iya sanya APC shan kaye a jihar.
Ɓarayi 5 sun 4 da ajalinsu a hannun wasu matasa a Kaduna, an ƙona 2 ƙurmus.
Shugaba Buhari ya ce gwamnati ta sayo jiragen yaki 23 domin kawar da Boko Haram.
An bayar da belin matar da ake zargi da kashe ‘ya’yanta a Kano bisa dalilin tabin hankali.
Wata kotu a Katsina ta jinginar da hukuncin da kotun Shari’a ta bayar na a kamo Mahadi Shehu.
Shugaba Buhari ya aikewa da Sanata Kwankwaso ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa.
An yi wa Yariman Saudiyya Muhammad Bin Salman allurar riga-kafin korona.
Jami’an tsaron Turkiyya sun kubutar da ‘yan gudun hijira cikin teku.
Mutane da dama sun mutu sakamakon kifewar jirgin ruwa a Kogin Albert kan hanyarsu na zuwa Congo daga Uganda.
Coronavirus: ‘Yan wasan Man City Jesus da Walker sun kamu.