An sami karin mutane 1,041 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya jimilla 81,963.
An saki Tsohon mai magana da yawun PDP, Oliseh Metuh bayan watanni 10 a tsare.
Ƴan bindiga sun kashe ƴan sanda uku a Benue.
Jam’iyyar APC ta ce nan ba da jimawa ba Najeriya za ta fita daga matsin tattalin arziki.
Boko Haram sun kai hari a garin Garkida da ke Karamar Hukumar Gombi ta jihar Adamawa a jiya.
Ƴan bindiga sun kashe mutum 8 da ƙona buhunan masara 330 Giwa ta jihar Kaduna.
Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti na musamman don yaki da yunwa a kasa.
Rundunar Sojojin Najeriya sun ce a shirye suke don kawo karshen Boko Haram a Jihohin Borno da Yobe.
Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, Mahaifin Tsohon Gwamnan Kano, Kwankwaso ya rasu.
Brexit: Boris Johnson ya yaba kan ƙulla yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Ingila da Tarayyar Turai.
Turkiyya ta yi nasarar gwajin harba makamin roka a karkashin teku.
Ana ci gaba da zanga-zangar neman Pashinyan ya yi murabus a matsayin Firaministan Armenia.