Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban kungiyar Jido Warrious dake Garin Jido a yankin karamar hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano Najeriya Auwalu Ashiru Jido ( A A Jido ) yace lokaci yayi da Gwamnatoci a najeriya zasu karfafawa masu kungiyoyin kwallon kafa na kashin kansu gwiywa dan ganin su cigaba da daukar dawainiyar matasa a harkokin wasan da sauran harkokin rayuwa,

A wata tattaunawa da yayi da sashin wallafa labarai na Express Radio 90.3 fm gabanin wani shiri na musamman da zai gudanar a tashar ranar Asabar da karfe 3:00pm AA Jido yace laakari da rawar da masu kungiyoyi ke takawa wajen bunkasa cigaban matasa a harkokin Wasanni akwai bukatar gwamnati da hukumomi su dinga zama da masu kungiyoyin kwallon kafa dan tattaunawa dasu kan yadda zaa hada karfi da karfe wajen shawo kan matsalolin dake damun alumma a irin wannan lokaci

A A Jido ya kara da cewa ba kowane Abu gwamnati ke iya fuskanta ba na matsalolin matasa amma wadanda ke jagorantar su a irin harkokin da matasan keda shaawa na da cikakkiyar masaniya kan bukatun matasan, inda yace inganta harkokin Wasanni kamar kwallon kafa zai kauda kaso 65 cikin Dari na matsalolin shaye shaye, Daba, Kwace da Zaman kashe wando da dinbin matasa keyi,

Dangane da yadda zaa kawo karshe matsalolin da lasafta A A Jido cewa yayi irin masu kungiyoyin kwallon kafa a jihar Kano Kadai sunfi 100,000 inda kowace kungiya keda yan wasa a kalla 40 da shugabanni a kalla 10 da yan kallo kusa 100 a kwace kungiya idan ka hada adadin zakaga akwai mutane masu yawa acikin harka kwallon kafa kadai banda sauran Wasanni amma abin takaici shine hukumomin dake da iko kan alumma basa duban irin yadda wadannan bangarori ke kokarin kare wadannan matasan,

Dabgane da yadda ya kamata gwamnatoci suyi Auwalu Ashiru Jido cewa yayi idan ka dubi irin kokari da hukumar kwallon kafa ta jihar Kano karkashin jagorancin Sharu Rabiu Ahlan keyi na shiga lungu da sako da fadada da bunkasa wasan kwallon kafa to akwai bukatar gwamnatin jiha da kananan hukumomi su karfafa wa hukumar ta kowane fanni musamman wajen tattaunawa da su kai tsaye da bibiyar irin kokarin da suke wajen kare matasa daga aikata miyagun ayyuka,

Da yake bayani kan yadda kananan hukumomi ke taka rawa wajen bunkasa Wasanni A A Jido cewa yayi akwai bukatar sake wayar da kan mahukunta a matakin kananan hukumomi dan su gane cewa wasannan yafi karfin wasan da suke tunani ya zama Sana’a da ake samun arziki mai tsafta da EFCC ba bibiyar sa saboda halaccin dukiyar da ake samu to dan haka shugabanni kananan hukumomi su tashi tsaye dan samarwa matasan su makoma a harkokin Wasanni,

Dangane da kungiyarsa ta Jido Warrious data ta kaiga wasan karshe a gasar cin Kofin Sanatan Kano Ta Kudu A A Jido cewa yayi ya zama wajibi ya jinjinawa yan wasa, shugabanni, Nagoya baya da dukka alummar Garin Jido bisa kokari jajircewa da adduoi da akayi tayi ba dare ba rana dan ganin munkai ga nasara gashi kuma Allah ya amsa duk da irin siyasar kwallon kafa munkai gaci muna godiya, amma fa aiki bai kare ba dan akwai wasan karshe kuma mai zafine kwarai amma ina da tabbacin cewa yan wasana na Jido Warrious Mayakan gaskene bazasu bani kunya ba, zasuyi nasara, Adduar kawai muke sake bukata, dan musamu wannan nasarar da kowa ke son gani,

A lahadin nan ce 28/12/2020 ake sa ran buga wasan karshe tsakanin Jido Warrious da Ganduje Babes a filin wasa na Kano Pillars dake Sabon Gari.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *