An sami karin mutane 1,133 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya jimilla 80,922.
Fadar Shugaban kasa ta ce ana shiryawa Buhari makarkashiya mai kama da juyin mulki.
Covid-19: Gwamnatin jihar Plateau ta ce ba za ta rufe jihar ba, sakamakon cutar.
Mutane 12 suka rasa rayukansu a wani mammunar hatsarin mota a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi tur da matakin Trump na yafe wa sojojin hayar Amurka da suka yi kisa a Iraƙi.
Wasu Mahara sun kashe mutum 90 a Ethiopia.
Shugaba Trump ya yi fatali da tallafin dala biliyan 900 da za a bai wa Amurkawa.
Coronavirus: Tunisia za ta ƙara tsawaita wa’adin dokar hana fita.
‘Yan bindiga a Afghanistan sun kashe shugaban kungiyar sa ido kan zabe mafi girma a kasar.
Iker Casillas ya koma Real Madrid a matsayin ma’aikaci.
EFL: Manchester United ta sami nasara a kan Everton da ci 2:0 a wasan jiya.
EFL: Tottenham ta sami nasara a kan Stoke City da ci 3:1 a wasan jiya.
LaLiga: Real Madrid ta sami nasara a kan Granada da ci 2:0 a wasan jiya.