Allah ya yiwa shahararren malamin nan na addinin Musulunci da ke Najeriya, Sheikh Ahmed Lemu rasuwa.
Shehin malamin ya rasu ne a safiyar yau Alhamis, 24 ga watan Disamba a garin Minna, babbar birnin jihar Niger, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.
Ya rasu yana da shekara 91 a duniya.
Daya daga cikin yayan marigayin, Nuruddeen Lemu, ya tabbatar da rasuwar mahaifinsu, inda ya ce idan anjima kaɗan za a soma shirye-shiryen binne shi.
Sheikh Dr. Lemu shahararren masani, ya kasance mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa ga yiwa musulunci hidima.