Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Jami’an hukumar yan sanda a jihar Kano sun damke wani mutumi mai suna, Adamu Musa, ‘dansa, sule Mallam, da jikansa, Isyaku sule, kan laifin kisan wani mutum da ake zargi da garkuwa da mutane.

Ba shi kadai suka kashe ba, sun hada da diyarsa mai shekaru biyar da haihuwa, wakilinmu Nazifi Bala Dukaws ya ruwaito.

Wannan abu ya auku ne a kauyen Gomo, a karamar hukumar Sumaila a jihar Kano.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, ya bayyana a ranar 26 ga Agusta cewa sun dira gidan mutumin mai suna Kabiru Yau, dake Madunkuri a garin Gomo kuma suka kashehi da diyarsa, Harira Yakubu.

Kakakin a jawabin da ya saki ranar Talata ta ce Malam Musa ya amsa laifin hannu cikin kisan kai.

Yace “ya umurci yaransa uku da jikansa su kashe mutumin kan zargin cewa yana garkuwa da mutane.”

Sun yi amfani da adduna da gorori wajen dukan mutumin da diyarsa har lahira, a cewar Kiyawa.

Ya kara da cewa an damkesu ne ranar 19 ga watan Disamba, kimanin kwanaki 119 bayan da suka aikata laifin kisan.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *