An sami karin mutane 356 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, jimilla 78,790.
Gwamna Zulum na jihar Borno ya ce gaskiya sojoji da ‘yan sanda da aka tura yankinsa sun ba shi kunya.
Covid-19: Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin rufe makarantu da wuraren shaƙatawa.
Wani bangaren jam’iyyar APC a jihar Rivers ta dakatar da Rotimi Amaechi daga jam’iyyar.
Gwamnatin tarayya ta ce kungiyar ASUU za su koma bakin aiki a watan Janairu 2021.
Wata kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin a saki Mubarak Bala, wanda yake cin zarafin addinin musulunci.
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama mutane 42 da laifin sayar da giya da karuwanci a jihar.
Hukumar EFCC ta kama ‘yan damfara ta intanet 32 a Legas.
‘Yan bindiga sun ɗauke wata mata da ɗanta da direban ‘yan sanda a Kano.
An kama ‘yar tsohon Firaiministan Ethiopia, Semhal Meles.
Dutsen Kilauea da ke jihar Hawaii ta Amurka ya dawo da aman ruwan wuta.
Dakarun Isra’ila sun jikkata Falasdinawa 5 a garin Nabulus da ke Yammacin Gabar Kogin Jordan.
EPL: Chelsea ta sami nasara a kan West Ham United da ci 3:0 a wasan jiya.
EPL: Burnley ta sami nasara a kan Wolverhampton da ci 2:1 a wasan jiya.