Bayan kwashe kusan shekara daya da kungiyar malamai masu koyarwa na jam’i’o’i suka yi a gida suna yajin aiki tare da hadin kan cutar korona, gwamnatin Najeriya ta ce tana sa ran malaman za su koma aji a watan Janairun 2021.
Ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige ne ya tabbatar da hakan a ranar Litinin, 21 ga watan Disamba.
Ya tabbatar da cewa sun kai wani mizanin daidaitawa da kungiyar malaman jami’o’in da ya kai kashi 98.
Ministan ya tabbatar da cewa ragowar kashi biyun ba wani abun dubawa ne, lamurra ne da za a iya hakuri da su.
A kalamansa: “Mun cika burikan ASUU kusan kashi 98. Dan ragowar abubuwan da ba a rasa bane.
“A don haka nake fatan cikin daren yau mu kammala sauran ayyukan da ya dace mu yi. Su ma suna da wasu kananun ayyukan da ya dace su yi da jama’arsu.
“A ranar Talata muke sa rana za mu hadu da rana sannan mu sake tattaunawa. Akwai yuwuwar mu kawo karshen yajin aiki idan muka hadu ranar talata .”