Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamnatin tarayya ta kakaba wasu sabbin dokoki yayin hauhawar yaduwar cutar korona a fadin kasar nan, Channels TV ta wallafa.

Boss Mustapha, wanda shine shugaban kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da korona, ya sanar da hakan a ranar Litinin bayan bayanin da yayi ga kwamitin a birnin Abuja.

Ya bayyana cewa wannan umarnin sun fito ne daga mashawarta inda aka mika su ga jihohi a kan a tabbatar da su na tsawo makonni biyar.

Sabbin ka’idojin sun hada da rufe dukkan mashaya, gidajen rawa da wuraren taro. Rufe dukkan wuraren nishadi a dukkan jihohin kasar nan da birnin tarayya.

An bukaci dukkan gidajen cin abinci da su rufe ban da wadanda ke samar wa mazauna otal, wadanda ba a ci a ciki da kuma masu kaiwa har gida.

Hakazalika, dukkan tarukan da suka hada da biki, siyasa, nishadi, motsa jiki, liyafar karshen shekara da sauransu duk kada su wuce mutum 50.

Gwamnatin ta takaita tarukan addinai da kada a wuce kashi 50 na wurin bautar sannan a kiyaye dokokin nesa-nesa da juna tare da saka takunkumin fuska.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *