Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

A yayin da ake tunkarar kakar wasan 2020/2021/kamar yadda hukumar dake shirya gasar LMC ta ambata,

Shugaban Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Surajo Shuaibu Yahaya Jambul yace lokaci yayi da masoya kungiyar zasu sake hade kansu Dan ganin kungiyar ta kai ga nasarar da ake bukata,

A wata tattaunawa ta musamman da yayi da yan jaridu marubuta labarin wasanni na jihar Kano Jambul ya bukaci samun cikakken hadin kan kungiyar da sauran alummar jihar Kano dan kai kungiyar gaci a kakar wasa mai zuwa, inda yace lokaci yayi da duk masu ruwa da tsaki zasu sake bada gudunmawarsu kamar yadda suka saba bawa kungiyar a irin wannan lokaci,

Da yake amsa tambaya kan kalubalen da kungiyar ke fuskanta shugaban ya koka da zagon kasa da yace wasu gungun mutane ke yiwa kungiyar dan ganin an samu koma baya inda yace kungiyar Kano pillars ta kowa da Kowa ce saboda haka akwai bukatar duk masu wannan aniya su sauya tunani, inda yace sam bazasu lamunci irin yadda ake yiwa kungiyar bita da kulli da zagon kasa ba a wannan karon

Dangane da shirin kungiyar na tunkarar wasan bana Surajo Jambul cewa yayi yaja kunnen yan wasan kungiyar dasu .maida hankali dan ganin sun sami nssara a wasannin su, inda yayi barazanar biyansu rabin albashi matukar suka kasa tabuka abin azo a gani a wasanni 4 na farkon kakar bana,

Da yake karin haske kan nasarori da shugabancin sa ya samu surajon cewa yayi dora kungiyar kan hanyoyin zamani na fanin sadarwana da samarwa kungiyar alkibla da makoma wajen kare hakkin mallaka da tallata ta a kafar sadarwa na daga cikin abin da yake alfahari dashi inda yace kawo iyanzu kungiyar ta tsare yin amfani da ita dan gina kai da wasu keyi da kungiyar,

Rusa team c nadaga cikin batutuwan da shugaban ya tabo inda yace an rusa kungiyar dan bada dama ga karamar kungiyar dake da register Junior Pillars damar taka rawa tare da bunkasa kananan kungiyoyin U-13 da U- 15 ,

Daga bisani ya yaba tare da taya murna ga sabon shugabancin kingiyar marubuta labarin wasanni ta jihar Kano tare da yin alkawarin yin aiki tare da kungiyar da samun nasarar da aka sanya gaba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *