Shugaba Buhari ya koma Abuja bayan ya dauki mako guda a Daura.
Rundunar sojoji ta ce su suka ceto yaran Katsina, ta karyata kungiyar Miyetti Allah da Gwamnoni.
‘Yan Boko Haram sun yi garkuwa da fasinjoji 35 a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.
Gwamna Matawalle na jihar Zamfara ya caccaki Jam’iyyar APC a kan zarginsa da zama jagoran ta’addanci a arewa maso yamma.
2023: Tsohon Sakataren NHIS, Usman Yusuf ya ce ba lalle ba ne a iya gudanar da zabe ba saboda matsalar tsaro.
Wata matashiya, ‘yar kunar bakin-wake ta kashe mutum uku da bam Jihar Borno.
Kungiyar AFENIFERE ta bayyana sace daliban Kankara da kubutar da su a matsayin babbar damfara da shirin wasan kwaikwayo.
Ana zargin tsohon shugaban ƙasar Afrika ta tsakiya, Francois Bozize da ƙitsa juyin mulki.
Switzerland ta amince da fara amfani da riga-kafin korona na Pfizer/BioNTech.
EPL: Liverpool ta sami nasara a kan Crystal Palace da ci 7:0 a wasan yau.
LaLiga: Atletico Madrid ta sami nasara a kan Elche da ci 3:1 a wasan yau.