
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce ya zuwa daren Laraba, an samu karin mutum 30 da suka kamu da cutar sarkewar numfashi ta korona a jihar.
Hakan na nufin adadin mutanen da ke dauke da cutar a Kano ya kai 427 tun bayan bullar cutar a jihar, sai dai kuma an sallami mutum 6, inda 13 suka riga mu gidan gaskiya.
Jadawalin jihohin da cutar ta bulla da hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya, NCDC ta fitar ya nuna Kano ce ta biyu a yawan masu fama da cutar bayan Legas mai mutum 1,308 da Abuja babban birnin kasar inda ake da mutane 316.
A ranar 11 ga watan Afrilu ne hukumomi a Kano suka sanar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar kuma tun daga wannan lokacin aka rika samun karuwar mutanen da annobar ta shafa, kuma ci gaba da gwaje-gwaje a jihar bayan an sami tsaiko ya sa an sami karuwar yawan wadanda ke dauke da cutar.
1 Comment